Sunayen Kofofin Aljanna Guda Takwas (8): Ma’anarsu da Ayyukan da ke Kaiwa Gare Su
Aljanna ita ce mafi girman ni’ima da Allah Maɗaukakin Sarki ya tanadar wa bayinsa masu imani. Wuri ne na jin daɗi, salama, da rayuwa ta har abada, wanda babu baƙin ciki, babu ciwo, babu tsoro. Duk wanda ya yi imani da Allah da ManzonSa (SAW), ya kiyaye dokokin Musulunci, sannan ya mutu a kan imani, Allah Ya yi masa alkawarin Aljanna.
A Musulunci, ba kofa ɗaya ce kawai ta Aljanna ba, a’a, akwai kofofi guda takwas (8), kuma kowane kofa na da mutanen da ake kiran su ta cikinta bisa irin kyawawan ayyukan da suka fi yi a duniya. Wannan yana nuna yadda Allah Ya buɗe hanyoyi da dama domin bayinsa su samu shiga Aljanna.
Hadisi Kan Kofofin Aljanna
An ruwaito daga Ubaadah bn Saamit (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Duk wanda ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, ba shi...
