Sunayen Soyayya Zafafa Da Masoya Ke Amfani Da Su
Haduwar farko a tsakanin masoya yakan iya kasancewa wani abu mai ban sha’awa da ɗan rikitarwa, domin a irin wannan lokaci mutum kan kasa fahimtar irin kalaman soyayya da ya dace ya furtawa wadda yake so. Duk da kasancewar soyayya tana fitowa ne daga zuciya, akwai wasu kalmomi da sunaye da ke da karfin bayyana yadda zuciya take ji fiye da magana kai tsaye.
A dukkan al’adu, musamman a al’ummar Hausawa, masoya suna da nasu hanyoyin nuna kauna. Daya daga cikin hanyoyin da suka fi sauki kuma suke da tasiri sosai shi ne amfani da sunayen soyayya zafafa. Wadannan sunaye ba wai kawai kalmomi ba ne, suna dauke da sako mai karfi wanda ke kara dankon zumunci, shakuwa da amincewa tsakanin masoya.
Dukanmu muna da sunayen da muke amfani da su wajen kiran masoyinmu. Wasu suna kiran masoyinsu da Hon...
